[Audio] Download Raddi Mai Taken ‘Babban Bola’ ? Sheikh Bello Yabo Sokoto
RIGIJI GABJI! LALLAI ZA’A ‘KARA MAIMAITA WATA RADDI KENAN MAI TAKEN BABAN BOLA KAMAR YADDA AKA YI NA MANI MAYE! TABBAS ASH-SHEIKH BELLO YABO SOKOTO YA KARKATO YEKUWAR MAGANARSHI IZUWA MASALLACIN SULTAN BELLO KADUNA. MAI GURI YA ZO, MAI TABARMA DOLE YA NADE. DON HAKA DOLE MU JANYE MU BAR MA MALLAM FAGEN.
!
Mu’uzilanci insha’Allah(T) karshen ki tazo a Sultan bello mosque kaduna
!
“Za mu yiwa Malam Bola raddi ba zamu kyale shi ba” inji Ash-Sheikh Bello Yabo Sokoto
Mallam yayi wannan jawabin ne jiya asabar a majalisin karatun shi asa’ilin da yake karantun littafin Attargib wattarhib.
Ga Kadan Daga cikin Abubuwan da Wanannan Goron Gayyata Ya kunsa kafin ku saukar da shi
!
ASH-SHEIKH BELLO YABO SOKOTO YACE; ” Duk Wanda ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad (SAW) manzon Allah ne toh shin ana cewa ga hadisi mallammai masana hadisi sun tabbatar da ingancinshi yace amma ai Mallam wa’ni bai ce haka ba ko kuma Mallam wa’ni bai yi aiki da hadisin ba?? Wai yanzu wassu mallammai aka sawa sharadi wai ko hadisi ya tabbata daga Annabi sai wai idan sunyi aiki dashi ko sun yi fatawa dashi. Toh kenan da wannan mallamin da manzon Allah (SAW) waffi wani girma?? Kenan in munka bi wanga ‘ka’ida kenan wannan mallamin ya fi manzon Allah (SAW) girma. Don haka wannan rashin sanin addini ne yaa ku jama’a, wannan rashin ganin girman Allah ne. Imamu Malik aka so a sanya mana wai bamu isa muyi aiki da hadisin Annabi ba wai sai Imamu Malik ya bada approval………….
!
Jama’a akwai ban mamaki mutumin dake iddia’in Sunnah ya ‘dauko ‘kiyayya ya ‘dora ma hadisan manzon Allah (SAW). Duk Nigeria Malamai na Sunnah da na bidi’a, mutumin da ya fito da hadisan manzon Allah (SAW) shine Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Allah yayi mishi rahama. Mallam kullum zai yi karatun hadisi taken da yake yi shine; Karatun hadisi da aiki dashi shine zaman lafiya ga musulmi. Toh yau ga abun mamaki wani wadda adda alaka dashi shi ke bude baki yana cewa karatun hadisi da aiki dashi shine fitina ga al’ummar musulmi. Jama’a akwai ban mamaki ko babu?? Allah ka shiryar da Baban bola.
!
Amma Baban bola ya ‘bace ‘bata mai nisa tunda yaddauko ‘kiyayya ya aza ma hadisan manzon Allah (SAW). Wallahi Tallahi Billahilladhi la’ilaha’illahuwa wannan ‘bata ce ba shiriya bace. Wannan Sharri ne ba alkhairi bane kuma abun bakin ciki ne gare mu baki ‘daya. Mun yi bakin cikin faruwar wannan lamarin kuma musamman ace a cikin zuri’ar Mallam Abubakar Mahmud Gumi ne anka samu wanga lamari akwai bakin ciki. Muna rokon Allah ka janye mana wannan fitinan kayi mana maganin wannan musibar. Kaga inda wani ne ba shi ba da sai muce ‘kiyayya yake yi ga da’awar Mallam Abubakar Gumi don haka da’awarce ta Mallam yake so ya karya. Mallam ya ce karatun hadisi da aiki dashi kaiko ka ce duk fitintunun da muke ciki duniyar musulunci ba abunda ya kawo fitintunun illa hadisan nan. Kenan yayi ma Mallam raddi ko bai yi ba?? Yayi ma Mallam RADDI mu ko zamu bashi namu. Allah ya sani muna girma Abubakar Gumi amma girman da muke gani na manzon Allah (SAW) ya fi na Abubakar Mahmud Gumi domin shima Mallam Abubakar Gumi ya samo na shi girman ne ta hanyar manzon Allah (SAW). Saboda girmama manzon Allah (SAW) da yayi shiyyassa munka girmamashi.
!
Toh wallahi ko wacce zai taba manzon Allah (SAW) toh wallahi bamu ganin girma nai kuma baza mu ‘kyale shi ba. Don haka wadannan tabargazozin da yayi wallahi zamu bi su ‘daya bayan ‘daya mu tarwatsa su baza mu ‘kyale su ba. Manzon Allah (SAW) ya fi kowa girma a wurin mu. Duk wanda ya nuna ‘kiyayya da hadisi zamu zare takobin ‘kiyayya da shi, kuma ‘kiyayya mai muni. Mai ya raba mu da ‘yan bidi’a da ‘yan ‘darika?? Ba ‘kiyayya ga Sunnah ba?? Sannan wani sai yazo don yana cikin mu ya ya’ki Sunnah kuma mu ‘kyale?? Wallahi baza mu ‘kyale shi ba.
!
……………………. An wayi gari wai hadisin Sitta shawwal ne Baban bola zai ce wai akwai gwaranci a cikin larabcin. Kenan Shi yanzu Baban bola ya hi Annabi iya larabci, ya hi Imamu Malik da ya kawo hadisin iya larabci, duk dattijan da ac-cikin isnadin hadisin haddasana fulan, an fulan, an fulan an ayyubal ansari duk ya hi su iya larabci duk Baban bola ya hi su iya larabci. In baccin wani abu sai ince sakaran banza. Allah ya shiryar damu! Allah ya shiryar damu!! Abunda na fadi daidai Allah ya bani lada da ni daku da kunka saurara. Inda kuskure ya auku Allah ya yafe mini ya share shi cikin zukatanku. Subhanakallahuma was bihamdika Ash’hadu anla’ilaha’illa anta Astagfiruka wa’atubu ilaik.
Latsa wanannan adireshi na kasa don sauraren somin tabin wanannan anticipate raddin, ko kuma ince Goron Gayyata Daga Bakin ASH-Sheikh Bello yabo Sokoto.
Download Audio Now
Sources: Engr Abu ibn Kamis