Uncategorized

Osinbajo Zai Ziyarci Jihar Katsina Don Kaddamar Da Asibiti

Osinbajo Zai Ziyarci Jihar Katsina Don Kaddamar Da Asibiti


…Zai kuma gana da ‘yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai kaddamar da asibitin matsakaita da kananan masana’antu (MSMEs) a yau Alhamis, a jihar Katsina a yunkurin bunkasa tattalin arziki da ayyuka a kasar nan.

Kwamishinan ciniki, masana’antu da yawon shakatawa na jihar Katsina, Alhaji Abubakar Yusuf ne, ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Katsina a jiya Laraba.

Kwamishinan ya ce a lokacin ziyarar, Osinbajo zai gana da ‘yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta da kuma yadda za a shawo kan matsalolin.

Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta riga ta kafa wani kwamiti don wayar da kan ‘yan kasuwa a kan muhimmancin ziyarar.

®Facebook/Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button