Uncategorized

MANOMI ZAI IYA SAYAR DA HATSINSA KAFIN YA GIRBE ?

MANOMI ZAI IYA SAYAR DA HATSINSA KAFIN YA GIRBE ? Tambaya: Assalamu Alaikum. Mutum ne yake bada kudin Gero ga manoma tun kafin ma amfanin ya girma. Misali, in ana saida Gero a lokacin shifka #450, to sai suyi lissafi akan tsammanin Geron zai sauko zuwa #150. Kaga duk #450 daya ba manomi, zai kawo mai Tiya 3 ta Gero kenan. Menene halaccin wannan ciniki ? Amsa: Wa alaikum assalam, Ya halatta mutukar sun cimma daidaito akan hakan, wannan shi ake kira Salam a wajan malaman Fiqhu(Kan ta gasu), Annabi (s.a.w) da ya zo Madina ya samu mutanen garin suna wannan cunikayyar, sai ya ce musu: (Duk Wanda zai yi, to ya yi a cikin Ma’auni sananne, zuwa lokaci sananne) . Allah ya halatta wannan nau’i na cinikayya saboda saukakawa mutane, Manomi zai iya bukatar kudi kafin amfaninsa ya zo. Allah ne mafi sani. Amsawa: Dr jamilu zarewa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button