Kungiyar Dattawan Arewa ACF Tayi Allah Wadai Da Hatsaniyar Dake Faruwa Tsakanin Gwamnatin Kano Da Fadar Masarautar Kano
Kungiyar Dattawan Arewa ACF Tayi Allah Wadai Da Hatsaniyar Dake Faruwa Tsakanin Gwamnatin Kano Da Fadar Masarautar Kano
Kungiyar ta bayyana hakanne a cikin takardar bayan taro data fitar jim kadan bayan kammala babban taro na kungiyar, wanda ya gudana a babban ofishin kungiyar dake titin Sokoto a garin Kaduna.
Dattawan na Arewa karkashin jagorancin shugaban kungiyar tasu Alhaji Ibrahim Commasie Sardaunan Katsina, sun bayyana cewar da akwai wasu makiya ne wadanda suka rura wutar rikici a tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Muhammad Sunusi II kuma abin bakin ciki ne faruwar haka ga dukkanin wani Dan arewa, inda sukayi fatan Allah zai kauda faruwar haka anan gaba.
Daga karshen taron kungiyar sun kara jaddada mubaya’arsu ga mai girma Shugaba Buhari tare da yin addu’ar Allah ya kara mishi lafiya da tsawon kwana, domin ya dawo ya cigaba da jagorar kasar bisa ga adalci kamar yadda ya saba.
Rahoto Daga :Aminiya