Uncategorized

Dattin Zina !!! – Sheikh Aminu Ibrahim. Daurawa Kano

Advertisment

Dattin  Zina  !!!


Tabbas ! Duk zuciyarda ta cudanya da zina, to
wannan zuciya ta zama mai ha’inci kuma
ma’abocinta bazai taba zama cikakken mumini,
har se in ya tuba.


Bincike ya nuna cewa, idan mace tayi nisa cikin
zina, to babu minti daya a rayuwarta face ta
aikata zina, ko sha’awarta ta taso, kuma idan
bata samu biyan bukata ba, takan shiga wani
mummunan hali. 


Haka shima namiji idan zuciyarsa ta cudanya da zina, to zuciyarsa takan kawo masa sha’awar yi
da muharramansa, kamar uwarsa data haifeshi
ko
qannensa mata, wani lokacin zuciyar kan qawata
masa sha’awarsu.


Zina mugun ciwo ne da yake kashe ma’abocinsa
ta ciki kafin ya fito waje.


Zina idan tayi nisa a zuciyar mutum takan lalata
zuriyarsa, koda bayan ransa, za’a dinga samun
masu irin halinsa mazinata.


Dan haka Manzon Allah S.A.W yace, “mai zina
ba
mumini bane, ai bashi da imani lokacinda yake
aikata zina”


‘Yan uwana, abokaina, mata da maza mu nisanci
zina, mu nisanci masu yinta, domin ita dabi’a ce
takanyi naso ne kuma matuqar kana tareda
mazinaci, to wataran shaitan zai qawata maka
sha’awar aikatata.


Ya Sarkin Sarakuna,
Ya Maji Roqon bayinsa
Ya Allah ka karemu da fadawa a cikin wannan
masifa, masuyi kuma Allah shiryesu su daina, ya
Allah gafarta mana zunubanmu .Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button