AddiniUncategorized

Duk Wanda Ba Ya Maulidin Manzon Allah (S.A.W) Ba Musulmi Ba Ne – Cewar Prof. Maqari

Duk Wanda Ba Ya Maulidin Manzon Allah (S.A.W) Ba Musulmi Ba Ne - Cewar Prof. MaqariDaya daga cikin ma su jan ragamar babbar masallacin Abuja, kuma babban malami mai bin darikar qadriyya, Prof. Maqari ya yi tsokaci akan tatamurzan bukin maulidin da a ka dade ana kumfar baki akai na nuna murna da samuwar fiyayyen halitta Manzon Allah (S.A.W) yanda ya bayyana cewa ai duk wanda ba ya maulidin, to shi ba musulmi ba ne.
A wani gajerin bidiyo da ya ke ta yawo a kafofin sada zumunta, jaridar Manuniya ta hango babbar malamin, mai bin darikar qadiriyya ya na furta cewa ai duk wanda ba ya maulidi, to shi ba musulmi ba ne.
A zancensa ya na cewa;”Duk wanda ba ya yin Maulidin Manzon Allah (S.A.W) ba Musulmi ba ne. Ina yawan fadin wannan, domin maulidi shi ne mujarradin murnar samuwar Manzon Allah (S.A.W). Da ka yi murna da samuwar Manzon Allah (S.A.W), ko cikin zuciyarka, ka yi maulidi – shi kuma ya ya ka aiwatar da murnar, shi ne a ke samun banbanci. Hanyar, ranar sha biyu ga wata a ciyar da abinci a yi kaza, wannan fahimtar wasu ne. Idan ka ce baka yarda da wannan hanyar ba, ijitihad…”
Maulidi dai buki ne da Al’ummar Musulmai su ke gudanarwa shekara-shekara domin nuna murnansu na samuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W). Amma, wasu kaso daga cikiñ Musulmai su na alakanta bikin da “Bidi’a” saboda Manzon Allah bai ce a yi ba kuma sahabbansa ba su yi ba.
A gefe daya kuma, akwai wanda su ka nuna yin maulidin ya na da kyau sai dai yanda a ke gudanar da shi ne yanzu Sam bai kamata ba; cakuduwar maza da mata ana rawa da rairaya da kuma samar da dandazon mutane ta hanyar yin ma su lakabi munana irinsu; Nigogin Manzon Allah, yan barandan Manzon Allah da dai sauransu.
Ga bidiyon nan kasa inda yake fadi haka.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA