Uncategorized
Fatawar Rabon Gado (95) Dr jamilu Yusuf Zarewa
Fatawar Rabon Gado (95)
Tambaya
Assalamu alaikum warahahamtullahi wabara katihu mutum ne ya mutu ya bar mata da yara 3, mata 2, namiji 1, sannan kuma mahaifi da mahaifiyar shi duk suna raye da wasu daga cikin yayyin shi.
Don Allah ya za’a raba gadon wannan mutum.
Amsa
wa’alaikum assalam to dan’uwa,za’a raba dukiyar da ya bari kashi ashirin da hudu ,a bawa matar kashi ukku na dukiya(Thumun), mahaifinsa a bashi kashi hudu (sudus),mahaifiyarsa a bata kashi hudu (sudus), yaran kuma a basu ragowar goma sha ukku duk namiji ya dau kaso mata biyu.
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
28/01/2017
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com