Labarai

Kotun daukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen cmrd Bashir umar Gorau ɗan majalisar tarayya

Advertisment

A yau din nan 16/12/2023 kotun daukaka kara ta tabbatar da zaɓen dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Goronyo/Gaba da ke gabascin Sokoto.

Bashir umar Gorau shine dan majalisar na farko dan aluta da ƙarancin shekaru ya samu tsayawa tara sau daya kuma yaci inda ya doke wani dattijo dan jam’iyar APC.

Kotun daukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen cmrd Bashir umar Gorau ɗan majalisar tarayya
Kotun daukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen cmrd Bashir umar Gorau ɗan majalisar tarayya

Shine cmrd Bashir Umar Gorau ya wallafa jindadinsa da godiya ga Allah akan nasarar da ya samu tare da jaddada godiya ga mai gidansa kuma ubansa tsohon gwamnan jihar Sokoto sanata Rt Aminu waziri tambuwal sanatan kudan cin Sokoto kamar yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.

Alhamdulillah ⚖️

Ina matukar godiya ga ɗimbin goyon bayan da muka samu tun farkon tafiyarmu har zuwa nasaramu yau a Kotun Ɗaukaka Ƙara. Ina mika godiya ta ga Babana Dattijo Sanata Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sokoto), bisa jajircewarsa da goyon bayansa. Ina mika godiyata ga ‘yan uwa na da ‘ya’yan jam’iyyar PDP da dukkanin al’ummomin mazabar Goronyo/Gada da suka tsaya tare da mu tun daga ranar farko.

Ina ba ku tabbacin cewa wannan nasara zata ƙara muna kwarin guiwar jajircewa wajen yin ayukka masu tasiri ga rayuwar jama’armu yadda ya kamata. Ina fatar zamu cigaba da wannan tafiya ta cigaba da hidima ga al’umma.

Nagode da amincewa da goyon bayan ku.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button