Labarai

Wallahi Duk Wadanda Suka Yaudari Mutane da Musulmi da Musulmi Sai Sun Hadu da Allah”, Mahdi Shehu

Advertisment

Fitaccen mai fafutuka, Mahdi Shehu ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima kan halin da yan kasar ke ciki Mahdi ya kuma bayyana cewa duk wadanda suka yaudari mutane suka tallata masu Tinubu da Shettima da sunan tikitin Musulmi da Musulmi za su je su tarar da Allah Dan kasuwar yana martani ne akan bidiyon wata tsohuwa da tace ta yi kuka da hawaye saboda rashin abinci da yunwa.jaridar liberty tvr na ruwaito.

Dan kasuwar Najeriya kuma mai fafutuka, Mahdi Shehu, ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda mawuyacin halin da mutane ke ciki a kasar. A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), Mahdi ya kuma caccaki wadanda suka tallata Tinubu da Kashim karkashin tikitin Musulmi da Musulmi.

An yaudari mutane da Muslim-Muslim, Mahdi Shehu Ya ce lallai sai Allah ya kama duk wadanda suka yaudari al’umma har suka zabi gwamnatin APC mai ci da sunan Musulunci.Wallahi Duk Wadanda Suka Yaudari Mutane da Musulmi da Musulmi Sai Sun Hadu da Allah”, 
Mahdi Shehu

Malaman addinin musulunci da-dama sun tallata tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima a yau kuma wasunsu suna kuka da gwamnati. Mahdi ya yi martani ne a kan bidiyon wata tsohuwar mata da ta koka tare da zubar da hawaye saboda tsananin yunwa.

Yadda tsohuwa ta yi kuka saboda yunwa A cikin bidiyon da ya daura a shafin nasa, an gano lokacin da wasu mata suka tsaya a mota suna rabawa bayin Allah abinci. Ko da suka bai wa wata tsohuwa nata kason a cikin wata yar leda, sai matar ta fashe da kuka tare da yi masu addu’a. An jiyo matar tana cewa:

“Har kuka na yi wa yunwa, lada kun gamu da shi girman Allah. Yanzu na yi kuka na gaji kan yunwa” Mahdi ya rubuta a shafin nasa: “Wallahi duk wadanda suka yaudari mutane suka saida Tinubu da kashim a karkashin yaudarar Muslim- Muslim sai sun hadu da Allah. “Ka ya nan sun saka mutane a cikin halin bala’i yumwa, taluci, fatara da.kuncin rayuwa, a lokacin da ake wadaka da satar sukiyar kasa. Allah ya isar mana.” Ga wallafar a kasa:

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button