Kannywood

Tsohuwar matar Adam a zango ta dawo fim

Advertisment

Amina Uba Hassan, tsohuwar matar fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango, ta dawo harkar fim a hukumance a matsayin babbar jaruma.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Amina wacce aka fi sani da Maman Haidar ta fara zama jaruma a Kannywood a farkon shekarun 2000 amma ta auri Zango a shekarar 2007.
Sai dai jarumar ta haifi da namiji a shekarar 2008 kuma auren nata ya samu tan garda bayan watanni biyar.
Bayan auren da ya yi rashin nasara, jarumar ta ci gaba da zama, sai dai ta sake fitowa a wani shiri na gidan talabijin na ‘Gidan Danja’ wanda kamfanin 2Effects ya shirya a kwanakin baya.
Kazalika Jarumar wacce haifaffiyar Kaduna ce tace ta dawo masana’antar fiye da yadda ta bari, kuma a wannan karon, sararin sama ne iyakarta.
Daily trust sun ruwaito cewa amina tace

“Yana da wahala sosai a matsayin ta na wacce ta haihuwa kuma bazawara ta sake komawa industry bayan barinsa na fiye da shekaru 10, zai da na tuntubi mutane da dama tare da juriya kafin na yanke shawarar. Babu shakka, yin fina-finai shine abin da na ke kaunar yi don haka zan cigaba da yi.”

Masoya sun yi ta yabawa rawar data taka a shirin da ake yadawa a tashar Arewa24.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button