Labarai
Rashin Imani: Yadda wata Kishiya ta askewa yar Kishiyarta kai kuma ta watsa mat ruwan Zafi (hotuna)
Yadda wata kishiya a jihar Sokoto ta askewa yar kishiyar ta gashin kai da kuma watsa mata ruwan zafi
Wannan yarinya mai suna Hafsat Marainiya ce, mahaifiyar ta ta rasu tsawon lokaci. Bayan rasuwar mahaifiyar ta ne kishiyar mahaifiyar ta ci gaba da azabtar da ita, ba dare ba rana tun tana karama.
Kololuwar rashin imamin da kishiyar mahaifiyar Hafsat ta yi wa Hafsat shine; Ta askewa Hafsan gashin kai, wannan ta zuba mata ruwan zafi tare da dukan ta.
Innalillahi wa inna ilahi raji’uun; Ashe ba a cikin dajin ne kadai ‘yan ta’adda su ke ba, har cikin gari akwai marasa imani da tausayi.
Ya Allah ka bai wa wannan yarinya lafiya.