Labarai

Sheikh Sudais ya kaddamar da mutum-mutumi da zai dinga tsaftacewa da raba ruwan Zam-Zam a Masallacin Manzon Allah

Advertisment

Sheikh Sudais ya kaddamar da mutum-mutumi da zai dinga tsaftacewa da raba ruwan Zam-Zam a Masallacin Manzon AllahKasar Saudiyya ta kaddamar da wani mutum-mutumi na zamani a Masallacin Harami ranar Larabar nan da ta gabata. Shugaban kula da al’amuran Masallacin, Sheikh Dr. Abdulrahman Bin Abdulaziz Al-Sudais shine ya kaddamar da mutum-mutumin.
An bayyana cewa mutum-mutumin da aka yi da fasahar zamani zai iya daukar ruwa mai yawan lita 68, kuma zai iya shafe awa hudu cur yana aiki, tare da zagaye wuri mai nisan mita 2,000 a kowacce sa’a daya.
Kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito, Dr. Al-Sudais ya bayyana cewa ma’aikatarsa tana kokari wajen aiki da bayyana abubuwan dake wakana. Hakan kuma na da nasaba da kokari da yake na gabatar da fasaha a manyan Masallatan biyu da za su yi daidai da zamani.
Hukumar Masallatan ta ce za ta yi kokari wajen tabbatar da cewa duka Mahajjata da masu zuwa Umrah sun samu tarbar da ta dace da zarar sun sanya kafar su a cikin Masallatan guda biyu.
Ana fatan ta hanyar samar da kwarewa mafi kyau, aikin hukumar Masallatan zai iya kawo martaba da wayewa ta masarautar wajen hidimar da ake yiwa Masallatan biyu masu alfarma da alhazansu.
Hakazalika, Dr. Al-Sudais bai manta da yaba ayyukan na’urorin mutum-mutumi na zamani ba da aka yi da kuma rawar da suke takawa wajen inganta tsarin hidimar da ake ba wa maziyartan Masallatan bisa sabbin ka’idojin kasa da kasa.

Masarautar ta kasar Saudiyya dai tabbas tana samun cigaba sosai tare da amfani da fasahar zamani don saukake ibadar maziyarta da mahajjata da suke zuwa aikin Hajji da Umrah, tare da kuma cigaba da bin matakan kariya da yaduwar annobar COVID-19.
Daya daga cikin amfanin da mutum-mutumin zamanin zai yi wajen inganta ayyukan Masallatan guda biyu dake da ban sha’awa, shine na’urorin za su dinga rabawa Mahajjata ruwan Zamzam, inda hakan zai taimaka wajen hana yaduwar cutar COVID-19 a tsakanin alhazai. jaridar Labarunhausa ne ta tattara bayyanin.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button