Harka ‘Crypto’ ya hana ma’aikatan asibiti kula da marasa lafiya a Gombe
Hukumar Gudanarwaar Asibitin Koyarwa na Jihar Gombe da ke Najeriya ta haramta wa ma’aikatan asibitin latsa wayoyinsu suna haƙar kuɗaɗen ‘Crypto’ a daidai lokacin da suke bakin aiki.
Hukumar Gudanarwar Asibitin ta ce, ta lura cewa, wannan sabon salon haƙar kuɗaɗen na Crypto na hana ma’aikatan kula da marasa lafiya.
Wata sanarwar cikin gida da asibitin ya fitar ta ce, ma’aikatan jinyar na da ƴancin gudanar da wasu ayyuka na daban, amma ba a lokacin da suke bakin aiki ba, kamar yadda RFIHausa na ruwaito.
Tuni asibitin ya baza wasu jami’ai da su sanya ido don tabbatar da cewa, ma’aikatan jinyar sun mutunta wannan umarni da aka ba su.
Hukumar Gudanarwar Asibitin ta ce, kula da lafiyar al’umma shi ne babban abin da ta sanya a gaba.
Wannan na zuwa ne a yayin da ɗimbin matasa a Najeriya suka rungumi aikin lallatsa wayoyinsu domin tara kuɗin Crypto ta yanar gizo, yayin da wasu ke caccakar su suna danganta hakan da lalaci.
Kodayake wasu masana na cewa, haƙar kuɗin na Crypto na da muhimmanci duba da cewa, duniyar tana ɗaukar sabuwar alkibila.