Addini

Na janye ƙara, amma na bar wa Allah – Farfesa Maƙari

Advertisment

Na janye ƙara, amma na bar wa Allah – Farfesa Maƙari
Na janye ƙara, amma na bar wa Allah – Farfesa Maƙari Hoto :freedom Fm

Babban limamin ƙasa da ke Abuja Farfesa Ibrahim Maƙari ya sanar da janye ƙarar da ya shigar da Dr. Abdallah Usman Gadonƙaya, sai dai ya ce ya bar wa Allah al’amarin.
Da yake zantawa da Freedom Radio, Farfesa Maƙari ya ce, ya janye ƙarar ne, sakamakon saka bakin magabatansa, ciki har da mahaifinsa.
Ya ce, dama an shigar da shari’ar ne a kotuna guda biyu, babbar kotu da kuma kotun shari’ar musulunci.
Amma kawo yanzu lauyoyinsa na ƙoƙarin janye ƙarar.
Farfesa Maƙari ya ƙara da cewa, ya barwa Allah, game da cewa ana da muryarsa yana kiran waya yana kare masu ɓatanci, kuma har yanzu yana ƙalubalanta kan a fito da muryar a cewarsa.
A ƙarshe ya yi kira ga ɗalibansa da ransu ya sosu, kan su yi haƙuri game da wannan matakin.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button