Ban taba tsammanin haka Ali Nuhu ya iya rawa ba – cewar Jarumar Nollywood (bidiyo)
Wata wakar sabon fim din jaruma Toyin Abraham, ‘The Ghost’” ta kayatar da mutane da dama don ‘yan uwanta jarumai sun nuna mata soyayya sosai a kafafen sada zumuntar zamani.
Wakar wacce ta sa abokan sana’ar ta suka yi ta kwasar rawa suna yin bidiyo, cikinsu kuwa ba a bar jarumin Kannywood, Ali Nuhu ba domin sai da ya gwada ta sa bajimtar.
Mabiyan Toyin kansu sun sha mamaki kwarai a kan rawan burgewar da Ali Nuhu ya kwasa bayan ita da kan ta Toyin ta wallafa bidiyon rawar nasa.
Legit hausa ta kara da cewa Jarumar Nollywood din ta yi iyakar kokarin ta wurin ganin cewa sabon fim din na ta na The Ghost ya kewaye ko ina a fadin kasar nan.
Fitacciyar jarumar wacce tauraron ta ya ke tsaka da haskawa ta saki wakar fim din kuma manyan sanannun abokan sana’ar ta suka dinga kwasar rawa don dai wakar ta kewaye ko ina.
A cikin shirin fim din, Ali Nuhu ya bayyana sannan ya tura wa jarumar bidiyon rawar da ya kwasar wa wakar sannan ta wallafa bidiyon rawar ta sa a shafin ta.
A cikin bidiyon, an ga yadda Ali Nuhu ya zage yana kwasar rawa irin ta zamani cike da burgewa. Har amfani yayi da hannayensa yayi yayin da wakar ta ke tashi.
Bayan wallafa wakar, jarumar ta wallafa cewa bata taba tunanin kwarewarsa a rawa ta kai haka ba.
View this post on Instagram