Addini

A karshe Sheikh Abdallah Gadon kaya ya nemi afuwa kan Zafaffan kalamansa kan prof MaQari

Advertisment

Jawabin wani bawan Allah kenan kan wannan bidiyo.
Na saurari bidiyon Sheikh Abdullahi gadon kaya a Lokacin da yake bayyana kuskuren sa Kan bidiyon hudubarsa ta Juma’ar data gabata Wacce yake kalubalantar Sheikh makari Kan Kalaman sa Kan Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara.
Wato Allah ya ga zuciyata na shiga cikin Farin Ciki a Lokacin da nake sauraron jawabin shehin malamin domin jawabi ne na Gaskiya na dubawa tare darasi musamman yadda yayi bayanin
Cewa a yanzu a hadin Kan Al’ummar musilmai shine mafi mahimmanci ba nuna kyama ga tsakanin Kungiyoyin Addinin Islamarmu ba.
Yadda wannan malami yaja kunne tare Jan Hankali ga batun hadin Kai shine mafi alkhari Ga Al’ummarmu ta islamar Arewacin Nageriya.
Allah ya Kara ganar da malamanmu damu baki daya
Allah ya kuma hada kanmu baki daya ya kara Mana soyayyar Annabi Muhammadu SAW…
Ga bidiyon nan kasa ku saurara.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button