Labarai

Gulum Ya Ziyarci Garuruwan Da Yan Boko Haram Nakai Hari Jiya Assabar

Advertisment

Jiya Asabar dab da goshin magriba karnukan wutar jahannama suka kaddamar da harin ta’addanci a garuruwa hudu dake karamar hukuma Hawul Jihar Borno
Yau Lahadi Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci inda harin ya faru
‘Yan ta’addan sun kashe mutane, sun kone makarantu da guraren ibada da ofishin jami’an tsaro, sun fasa shaguna gaba daya sun kwashe kayan dake ciki, sannan sun wawushe kayan abincin amfanin gona na mutanen garuruwan da suka noma
Harin ya faru ne a garuruwan Tashan-Alade, Shafa, Azare, Sabon-Kasuwa da Debro karamahar hukumar Hawul duk a daren jiya
Gwamna Zulum ya bada umarni nan take a fara sake gina makarantu da dakunan bauta da ofishin ‘yan sanda da shagunan da ‘yan ta’addan suka lalata
Na shafe kusan sati guda kullun sai ‘yan ta’adda sunyi harin ta’addanci a Borno, Yobe da Adamawa, kama suna neman sake farfadowa, wallahi akwai matsala a bangaren hada bayanan sirrin wadannan miyagun mutane, ya kamata Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta tashi tsaye
Allah Ka kawo mana karshen wannan masifa Datti Assalafy ne ya tattara bayyanai.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button