Labarai

Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa

Advertisment

Wata Babbar Kotun Jiha, mai zaman ta a sakatariyar Audu Bako a Jihar Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta yanke wa wani matashi, Sagiru Wada hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa.

A yayin yanke hukuncin a jiya Laraba, Mai Shari’a ta yi karatun baya, inda kuma ta samu matashin da laifin daddatsa kishiyar mahaifiyarsa da adda, inda ta kuma yanke masa hukuncin kisa, karkashin sashi na 221 na kundin dokar laifuka na Kano. Daily Nigerian Hausa

Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa
Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa

 

Kotun ta ce ta gamsu da tuhumar da ake masa bayan samun cikakkun shaidu, ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Advertisment

Tun da fari, an gurfanar da Wada bisa laifin kashe kishiyar mahaifiyarsa, Zainab Dan-Azumi da wata adda shekaru 8 da suka gabata.

Lauyan wanda ake ƙara, Barista Rabi’u Abubakar ya shaida wa kotun cewa matashin bashi da lafiyar ƙwaƙwalwa, amma kotun tai watsi da wannan rokon bisa cikakkun shaidu da tayi amfani da su.

Lauyan gwamnati, Barista Tijjani Ibrahim ya ce kotu ta yi nazari ta ga babu wani dalili da za a ce yana da motsi a ƙwaƙwalwar sa kuma hakan bai gamsar da ita ba, inda ta yi watsi da rokon.

Shi ma lauyan wanda ake ƙara ya ce za su zauna su yi nazari kuma su ga mataki na gaba da za su ɗauka.

Ali Mandawari, ɗan uwan marigayiyar ne, ya ce sun yi farin ciki da hukuncin kuma gaskiya ta yi halin ta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button