Mijinta ya koreta saboda ta musulunta, Yan uwa Musulmai sun taimaka mata (bidiyo)


Alhamdulillah ina cikin matukar farin cikin yadda yan’uwa musulmai suka nunawa Khadija gata, bayan da aka koreta aka wulakantata, kudin da kuka tara mata mun sai mata kayan abinci da katifar kwanciya Dubu Dari Uku (300k) mun sai mata gawayi da dankali na sanaar da za ta yi Dubu Casa’in (90k), mun kama mata haya Dubu Dari Biyu da Ashirin (220k) ga kudi da muka bata a hannunta, wasu kuma sun yi alkawarin za su aiko mata da kayan sakawa ita da yarta, muna adduar Allah ya faranta muku, na rasa da bakin da zan muku godiya ma.
MUNA ROKON KOWANNE MUSULMI KO BASHI DA KUDIN DA ZAI TAIMAKAWA BAIWAR ALLAH NAN YA TAYAMU YADA VEDIO DINTA TA SAMU TAIMAKON ADDININ DA AKA WULAKANTATA SABODA SHI
Zama ne ya kawo su Kano da mijinta sai take shaawar addinin musulunci, lokacin da ta furtawa mijinta za ta shiga yace sai dai tabar masa gida, ta amince da hakan sai ya koreta ya kwace yarta gashi tana dauke da tsohon ciki, ta rasa ina zata dinga kwana sai a soron makota, bata damu da halin da take ciki ba ta je Hisba ta sharada ta amshi addinin musulunci, kwana biyu da amsar addini nakuda ta kamata jamaar unguwar suka dauketa suka kaita asibitin Jakara saboda nakudar ta zo da matsala, acan asibitin ma tasha wahala ta zubar da jini, likitocin da kansu suka taimaka mata da jini da magani, bayan an sallameta sai makociyarta ce ta bata guri suke kwana a dakinta, itama saboda mijinta ba ya gari ya rafi cirani, a haka baiwar baiwar Allahnan ke wuni babu abinci ga jego ga rashin jini.
Bayan ta musulunta an saka mata suna Khadija, ita kuma diyarta ta saka mata Nana Aminatu mahaifiyar Manzon Allah Sallallahu alaihi, wannan baiwar Allah tana cikin damuwa domin mijinta ya dauke yarta babbar ya bar unguwar, ga jaririyar dake hannunta babu lafiya itama haka, yanayinta ma ya nuna kamar depression na bayan haihuwa ya kamata, babu gurin zama tunda dole idan mijin matar ya dawo tabar dakin, babu abinci, kayan jikintane kawai kayan da take da shi ga yarta babu lafiya, wannan aikin namu ne yan’uwa musulmi mu nunawa baiwar Allah nan gata mu kama mata gida mu bata sana’a mu karfafeta don Allah don da Annabinsa Sallallahu alaihi wasallam da addininmu da ta shigo mu fitar da ita daga cikin damuwa.
Ga wanda za su taimakawa baiwar Allah nan za su iya saka taimakonsu ta account din mu.
Account Number: 0109299375
Account name: Creative Helping Needy Foundation
Bank name: Access bank.
Ko
Account Number: 0127121207
Account name: Fauziyya Danladi Sulaiman
Bank name: Gt bank.
Ga masu neman karin bayani za su iya tuntubarmu ta WhatsApp ko message ko kiranmu ta wannan lambar waya 07037147070.
Don Allah mu taimakawa baiwar Allah nan ko da yada halin da take ciki ne har Allah yasa a samu taimakon da za mu iya mata.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




