Labarai

Dangote ya sake rage farashin litar man fetur saboda bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara

Advertisment

Kamfanin matatar Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N899.50k a kowace lita.

Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata takarda da aka fitar da safiyar Alhamis.

Kamfanin ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne domin “bada sauki ga ‘yan Najeriya kafin lokacin bukukuwan karshen shekara.”

Matatar mai ta farko mai zaman kanta a nahiyar Afrika, wadda a baya ta rage farashin zuwa N970 a kowace lita a ranar 24 ga watan Nuwamba, yanzu ta sanar da sabon farashi na N899.50k a kowace lita.

Advertisment

“Wannan ragin farashin an yi shi ne da nufin rage kudin sufuri a lokacin bukukuwan karshen shekara,” in ji sanarwar da Babban Jami’in Yada Labarai na Kamfanin, Anthony Chiejina, ya sa hannu.

~Daily Nigerian Hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button