Labarai

Yadda mai babbar mota ya kashe amarya tana bisa hanyar zuwa dakin Mijinta

A jiya lahadi wani mummunan al’amarin ya faru a garin kware karamar hukumar mulkin jahar sakkwato inda wani mai babban moto kirar valvo ya kashe amarya tana bisa hanyar zuwa kaita dakin mijinta.Yadda mai babbar mota ya kashe amarya tana bisa hanyar zuwa dakin Mijinta
Mai motar ya tuko motar ne daga mieyami da ke kasar niger daya daga cikin fasinja ya tabbatarwa da Hausaloaded cewa mai motar ya taso daga miyami babban birnin kasar niger cewa motar babu burki kuma sitarin motar baya juyawa idan ta tafi ta tafi ne.
Da sunka shigo nijeriya a karamar hukumar tangaza da ke sakkwato ya buge rakumi wanda ya shaida mana cewa tun daga nan tsarar rakumin ta kare,to shine fasinja da wani abokin tafiyarsa sunka sauka daga motar duba da motar babu lafiya sunka hau mashin.
Motar taci gaba da tafiya domin cikin garin sakkwato zato shigo shigowarsu cikin garin kware ke da wuya sainga motar amarya yana gudane to daman babu burki nan take ya murkushe motar da amarya ke ciki za’a kaita dakin mijinta rai yayi halinsa.
Allah ubangiji ya jikan amarya ya baiwa angonta hakuri da iyayenta da yan uwanta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button