Labarai

Yadda Al’ummar Garin Shasha Ta kasar Kongo ke neman fitsari Ruwa a jallo

Shasha, wani kauye ne a cikin yankin Masisi, mai tazarar kilomita 30,wanda yake kudu maso yammacin birnin Goma, babban birnin Kivu a Jamhuriyar Kongo.
Noma ya kasance daya daga cikin manyan Sana’o’i da al’ummar yankin Shasha ke yi, amma a yanzu sauran sun kasance suna kara samun raguwar aikin noma.Labarunhausa na ruwaito

RaShin isashen taki shi ya yi sanadin fara amfani da fitsari

Lamarin ya faru ne saboda karancin taki da al’ummar garin shasha ke fuskanta inda hakan ya haifar da nakasu wajen samun isassun amfanin gona da ake nomawa a yankin, wanda rashin samun isasun taki yasa basa iya noma abinda suma zai ishesu har su iya bawa makwabtan garuruwa saboda garin shasha ya kasance a baya yana wadata manyan garuruwa kamar Goma, da kayan masarufi.

Screenshot 20220504 1047262

Sun yanke shawarar fara amfani da fitsari

Domin shawo kan wannan matsala,Mazauna garin suka yanke shawaran fara amfani da fitsarin dan Adam inda yawancin manoman suke sayen fitsarin daga mazauna garin Shasha har ma dana makwabtan garuruwa, suna amfani da fitsarin ne a matsayin takin gargajiya.
Paul Kanyama, Wani mazaunin garin kuma manomi wanda ya kasance daya daga cikin sahun farko da suka fara amfani da fitsarin a matsayin taki a garin na Shasha.

Da farko muna zagaye gonakin mu da igiyoyin shuka,sannan sai mu rika fesa fitsarin, wanda yana da karfin da zai iya kaiwa kimanin wata daya yana amfani a gona inda yake kashe duk wasu kwarin da za su iya afkawa shuka, daga nan kuma sai mu sanya iri a gonakinmu kafin a yi feshi a karo na biyu. Wannan hanya ce da muke samun sakamako mai kyau domin kuwa amfanin gonakinmu ya na albarka” kanyama ya shaida.

Matasan garin hakan ta zame musu sana’a

Yayin da manoma garin Shasha ke cigaba da wannan al’ada ta amfani da fitsari a gonakinsu, su kuma matasan garin,ta zame musu hanyar samun kudi inda suke sayar da fitsarin su a gwangwani mai cin lita 20 a kan kudin kasar Kongo, Congolese francs 12,000, wato dalar Amurka 6.
Kahindo Lubuto Mwajuma, tana daya daga cikin matasan kauyen da suke sana’ar sayar da fitsari ga manoma.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button