Labarai

Asirin mai baiwa yan bindiga bayanan sirri ya tonu a katsina akwai ban mamaki

Advertisment

Asiri dai Sai ƙara Tonuwa yake, Sunan shi Alahaji Salisu ɗan garin Runka ne dake ƙaramar Hukumar Safana ta jihar Katsina, An kama shi da laifin bawa yan ta’adda Bayanan Sirri ‘ kamar yadda ya faɗa ba Bakin shi, yace shi ya Turo ɓarayi har Sau biyu a Garin Runka,

Abun Baƙin ciki anyi Garkuwa da ƴan garin shi an karɓi kuɗin fansa Har Naira miliyan 25 Amma an bashi dubu Ɗari 4, ya lissafa Manyan ƴan ta’adda har 3 waɗanda yake aiki tare dasu ‘ Sannan ya faɗi wani Mutum ɗaya da Suke aikin bada Bayanan Sirri ga ƴan ta’addan Tare, wanda yace an Basu Dubu Ɗari 8 sun Raba kowa Ɗari 4

Allah ta’ala yasa a yanke mashi Hukunci daidai Abunda ya aikat ya ƙara Tona Ma duk masu hali Irin Nashi Asiri,

????Ga Bidiyon Mai Baiwa ƴan ta’addan daji Bayanan Sirri Wanda aka kama a yankin ƙaramar Hukumar Safana ta jihar Katsina, Waƙa bakin mai ita Hausawa suka ce tafi daɗi ku saura Kuji

29/10/2024
Yarima Bk Dtm

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button