Alhamdulillah an saki Seaman Abbas soja mijin Hussaina (bidiyo)


A yau din nan da ake shiri a talabijin na Brekete family tv inda matarsa Seaman Abbas Hussaina tare da shi a gidan rediyo.
Tabbas wannan rokari shugaba ordinary president Ahmed Isah yayi namijin rokari na ganin cewa matar seaman Abbas taga mijinta kuma tana tare da shi a halin yanzu.
Zuwa anjima zamu kawo muku cikakken bayyani akan fitowar seaman abbas.
Ga bidiyon nan ku kalla.
Murjanatu Dirin Daji dake birnin Kebbi da ke arewacin Najeriya itama ta tofah albarkacin bakinta na irin ganin namijin kokari da Brekete Family Tv da mutane sunkayi na addu’ar Allah ya kuɓutar da seaman Abbas.
Ga abin da take cewa.
“Alhamdulillah naji dadi kwarai da samun yanci da Seaman Abbas yayi. Saidai mganar gaskiya an zalunci Abbas. Muna addu’ar Allah ya kiyaye afkuwan hakan a gaba.Ta tabbata idanhar kai talaka ne a Nijeriya ba kada wani gata kuma sai na Allah.
In Sha Allahu daukaka da haske na alheri mai tarin yawa na nan tafe ga Seaman Abbas. Saboda a tarihin duniya da yawan wadanda aka wulakanta, aka kaskanta, aka ci zarafinsu sun samu daukaka. Babban abun farin ciki soyayyarda Abbas da matarsa suke nunama junansu abun burgewa da daukar hankali ne. Allah shine gatan Abbas, In Sha Allahu kuma zai kawo masa mafita. Abbas bai zalunci kowa ba shine aka zalunta. Yanzu ne ya kamata mutane su taimaka masa, yanzu ne ya kamata mutane su tara masa kudi.
Muna kara neman alfarma ga Malaman mu na addinin musulunci kamar yarda suke kokari babu dare babu rana, su kara sa bakinsu a zaluncin da aka yiwa wannan bawan Allah. Duk wanda keda hannu a zaluntar wannan bawan Allah da ahalinsa, Allah yabi masa hakkinsa. Allah ya kawo mishi mafita. Allah ya buda masa wata hanyar wacce zai cigaba da tallafa ma iyalinsa. Allah ya bashi fiyeda abunda ya rasa.”