Labarai

Ba da son Buhari aka garkame iyakokin Najeriya ba – Ministar kudi

Advertisment
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna tirjiya game da rufe iyakokin Najeriya da makwabtanta saboda yana sane da matsanancin halin da tattalin arzikin kasashen zai shiga, don haka da farko bai amince da matakin ba, ini rahoton Daily Nigerian.
Majiyarmu ta ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba yayin da take ganawa da manema labaru a babban birnin Washington DC na kasar Amurka inda tace an dauke matakin ne don gyara alakar Najeriya da makwabtanta.
Hajiya Zainab tace bankin lamuni na Duniya, IMF na goyon bayan wannan mataki saboda tana sace da cewa ba wai an dauke shi bane da nufin kuntata ma kasashen, sai dai kawai domin yin gyara ne ga tsarin alakar kasuwanci tsakanin kasashen.
“An yi ta kokarin daidaitawa tsakanin Najeriya da sauran kasashen, amma abin ya ci tura, mun san akwai matsi ga tattalin arzikin kasashensu saboda wan nan mataki, amma abinda muke so kasashen nan su gane shine cewa zasu iya turo mana kayayyaki, amma fa sai ta tashoshin jiragen ruwanmu.
“Dolene kayan su shigo Najeriya cikin sundukai domin baiwa hukumar kwastam ta Najeriya daman bincikarsu, sa’annan kuma su dinga biyan duk harajin daya kamata, amma ba abinda suke yi ba kenan. Sai su bari a bude sundukai a kasashensu, sa’annan a shigo da kayan zuwa Najeriya ta barauniyar hanya.” Inji ta.
Daga karshe Ministar tace Najeriya ba zata bude iyakokinta ba har sai kasashen sun amince da bin tsarin cinikayya da kasuwanci na kungiyar kasashen yammacin Afirka, sa’annan ta kara da cewa har yanzu ana cigaba da tattaunawa a kan hakan.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button