Labarai

Bidiyo Wani Dattijo yayi Wuff da Wata zankadediyar yarinya ya tayar da kura a social media

Jama’a a soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da hoto da bidiyon wasu ma’aurata sabbin aure.

Angon wanda shekaru suka dan fara ja masa ya yi wuff da wata tsaleliyar budurwa danya shakaf.

Legit na ruwaito wannan labari tazarar shekaru da ke tsakanin sabbin ma’auratan shine abun da ya fi jan hankalin jama’a zuwa wurinsu inda sam wannan al’amari bai yi wa wasu dadi ba.

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya kuma shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram ya nuno inda ango ke bude kan amaryarsa cike da farin ciki da zumudi.

Mutane da dama sun ce a ganin farko da suka yi wa hoton, sun zata uba ne da ‘yarsa suke bankwana yayin da za a kaita dakin aurenta sai dai labari ya sha banban duba ga yanayin abubuwan da suka faru a bidiyon.Bidiyo Wani Dattijo yayi Wuff da Wata zankadediyar yarinya ya tayar da kura a social media

Mutane da dama sun ce a ganin farko da suka yi wa hoton, sun zata uba ne da ‘yarsa suke bankwana yayin da za a kaita dakin aurenta sai dai labari ya sha banban duba ga yanayin abubuwan da suka faru a bidiyon.

Martanin jama’a

Legit.ng Hausa ta zakulo wasu daga cikin martanonin da jama’a suka yi a kan wannan aure a kasa:

sadia_nas ta yi martani:

Masu cewa ai aure ne, sunnah aka raya ya fi a kama ma ta hotel, ku dubi yarinyar nan ku dubi shekarun mutumin nan me yasa bai samo bazawara ba ko wata babbar mace? ko wadda Mijinta ya mutu? ku gaya ma ni a gidan Ubanwa su ka dace?? Wallahi ku ji tsoron Allah, ko a musulunci akwai inda a ke gargadi akan irin wannan auren…a ina zai iya da yarinyar nan? don dai shi namiji kullum a rayuwa shi a ke favoring? comment kuma sai mun yi, wanda ya ce a yi posting a social media .”

zarah_duchess ta ce:

AMARYA ALLAH YA BAKI IKON DAUKAR KAYA.”
_zainiiiii ta yi martani:

Tsakani da Allah wanan ba daidai bane bata yi kama da tana farin ciki ba mtswwww.”
walinsky9 ya ce:

“Yafi Wanda suke kai kamarta hotel. Ayi ahankali don sunnah ya raya kar a kauce layi.”
aishashaheeda ta ce:

“Ko kunya babu. Tsoho kato dakai, kaje ka auro yarinyar da bata wuce yar cikinka ba. Kayan bacin rai.”

la_eeeshars_kitchen ta rubuta:

“Allah mun gode maka da ka bamu iyaye na gari masu hangen nesa.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button