Yanzu Yanzu : shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi da muƙarabansa sun rasu a hatsarin jirgi


Kamar yadda muke samun rahoto daga wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta fitaccen marubucin akan al’amaran rashin tsaro a Najeriya Mustapha sarkin kaya ya kawo rahoton mutuwar shugaban kasar da makarabansa.
Dukkan wadanda suke cikin Karamin jirgi Mai saukar angulu dake dauke da shugaban kasar Iran Ibrahim raisi sun rasu.
Wadanda suka rasun sun hada da shi kanshi shugaban kasar Iran din
IBRAHIM RAISI Shugaban kasa
– minister harkokin waje Amir Abdollahian
– Gwamnan gabachin Azerbaijan Malek Rahmati
– Tabriz’s Imam Mohammad Ali Alehashem
Matakin jirgin da maitaimaka masa
-shugaban masu hadiman cikin jirgin
-baban dogarin shugaban kasar
– dakuma maikula da lafiyarsa.








Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Mokhber ne yagaje shugaban kasar a matsayin sabon Shugaban kasar Iran.
ALLAH ya gafarta masu .
Majiyarmu ta samu karin bayyanin tabbacin mutuwar Ibrahim raisi a jaridar TRT AFRIKA HAUSA cewa
“Shugaban Iran Ebrahim Raisi da Ministan Harkokin Wajen ƙasar Hossein Amirabdollahian sun mutu sakamakon hatsarin jirgin helikwafta, kamar yadda wani jami’in gwamnatin ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






