Labarai

Miƙewar mazakuta sama da mintuna 30 illa ce ga maza – Binciken masana

Farfesa Ademola Popoola na Sashen tiyata na Jami’ar Ilorin, Unilorin, ya yi gargadin cewa miƙewar azzakari sama da mintuna 30 a yayin jima’i ba shi da amfani kuma na haifar da illa ga maza.

Popoola ya yi gargadin ne a Ilorin a lokacin gabatar da maƙala mai taken “Ubangiji ya sa mu yi fitsari lafiya”, a yayin taron lakca karo na 250 a jami’ar.

Miƙewar mazakuta sama da mintuna 30 illa ce ga maza, Likita ya yi gargaɗi
Miƙewar mazakuta sama da mintuna 30 illa ce ga maza, Likita ya yi gargaɗi

Daily Nigerian hausa na ruwaito,A cewarsa, “wanda azzakarin sa ya mike sama da mintuna 30, to ya gaggauta zuwa asibiti”.

Ya bayyana cewa dole ne a samu kwararren likita ya saukar da azzakarin idan ya mike sama da mintina 30 domin gujewa dena tashin sa.

Masanin, wanda ya lura cewa azzakari yana bukatar ya kasance mai kauri ko kuma a tsaye don samun gamsarwa ta jima’i, duk da haka, ya ce azzakari yakan karye ko ya yi targade.

“Bincike ya nuna cewa gefen dama na azzakari ya fi karye wa fiye da gefen hagu,” in ji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button