Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta gargadi jam’iyyun siyasa kada su sake su baiwa wani dan cocin Redeemed Church of Christ Group (RCCG) tikitin takara a zabe.
MURIC ta yi wannan gargadi ne a jawabin da shugabanta na shiyar Bauchi, Safiyanu Gambo, ya saki ga manema labarai.
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, wanda har yanzu bai bayyana niyyar takararsa ba babban Fasto ne a cocin RCCG, shafin daily news hausa.
Ana kyautata zaton cewa nan ba da dadewa ba zai ayyana takararsa.
A cewar MURIC, Cocin RCCG na son ganin bayan Musulunci a Najeriya kuma duk Musulmin da ya goyi bayansu makiyin addini ne.
Tace: “Wajibi ne mu hada kai kafin RCCG ta kawar da Musulmai da sauran darikokin Kirista.”
“Abinda yan uwa Musulumai ke fuskanta a kasar Yarbawa inda ake mayar da su saniyar ware duk da sune mafi rinjaye ya isa izina garemu mu san cewa idan yan cocin RCCG suka zama masu mulkin kasar nan.”
“Mu a Arewa muna lura da wannan abu. Ba zamu taba yarda dan cocin yaci zabe ba.”
Advertisment