Wasu Mazauna ƙauye sun cinye giwar da ta gudu daga gandun daji
Mazauna wani ƙauye da ke maƙwaftaka da gandun dajin Virunga a Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Kongo sun kashe tare da cinye wata giwa da ta fito daga gandun dajin.
Malaman daji sun ambato mazaunan ƙauyen da ake kira Katwiguru, waɗanda ke cike da murna na cewa “wannan tamkar nama ne daga sama gasasshe.”
Ƙungiyar masu aikin kare gandun dajin sun wallafa a shafinsu na tuwita cewar babu tabbas kan ko ƴan tawaye ne suka kashe giwar ko kuma mazauna ƙauyen.


Kafar yaɗa labaru ta BBCHAUSA ta ruwaito cewar a makonnin da suka gabata ne wasu matasa suka lalata shingen gandun dajin, lamarin da ya bai wa giwaye biyu damar ficewa.
A yanzu ba a san wane hali ɗaya giwar take ciki ba.
Virunga, wani shahararren gandun daji ne da ke tsakiyar yankin da ke fama da rikici kusa da iyaka da Uganda da kuma Rwanda.
Shafin gandun dajin ya ce giwaye 589 ne suka shiga gandun dajin a shekarar 2020, lamarin da ya sanya yawan giwayen da ke cikin gandun dajin ya kai 700.