Za mu Fitar da bata-garin cikin mu – MD Karota
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jiha KAROTA ta ce ya zama wajibi ta dauki matakin fitar da bata-garin cikinta domin inganta ayyukan Hukumar.
Shugaban Hukumar Karota Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a wannan rana ta Alhamis lokacin da ya bayar da umarnin tsare wasu Jami’in KAROTA wadanda ake zargi su da matsawa direbobin mota da karbe-karben kudi a wajen su.
Yace Hukumar baza ta zuba ido ta bari a sauke tsarin da aka kafa Hukumar a kai ba, a don haka ya zama wajibi a hukunta duk wanda aka samu da sauya salon aikin Hukumar.
Yaja hankalin direbobin mota da su guji bawa Jami’in hukumar ta KAROTA cin-hanci domin baya daga cikin manufar kafa Hukumar.
Ya kuma kara da cewa abinda ake bukata a wajen kowanne direba ya shi ne tabbatar ya mallaki dukkan takardun toki kafin ya hau kan titi, da kuma bin dokokin hanya a lokacin da ake tokin.
Daga karshe shugaban ya godewa wasu daga cikin Jami’in Hukumar bisa namijin kokarin da suke yi wajen aiki tukuru tare da tsare mutuncin ayyukan Hukumar.