Wata sabuwa ! Matar Aure takai mijinta kotu saboda yayi kokarin Cire NiKaf don yaga Fuskantar ta
Wata mata ‘yar kasar Saudiyya ‘yar shekara 50 ta kai karar mijin ta a kotu tana neman a raba aurensu saboda mijin nata ya bude mayafinta (Nikaf) a lokacin da take cikin barci domin ya kalli fuskarta.
Majiyar Taskar Labarai ta ruwaito tsawon shekaru 30 da aurensu, amma matar ba ta taba nuna fuskarta ga mijin nata ba, kamar yadda al’adar kauyensu a garin “Khamis Mushat” ta ke a kasar Saudiyya.
Taskar Labarai ta ruwaito a wannan al’adar miji baya ganin fuskar matarsa dole ne ta kasance a cikin nikabi a koda yaushe, “Saboda haka a karshe dai dole mijin ya nemi gafararta, ya yi alkawarin ba zai sake yin haka ba” a cewar kafar yada labarai ta NBC da Daily Mail
An ruwaito matar cikin fushi tana cewa “Bayan duk wadannan shekaru da muka kwashe, sai yanzu yake kokarin aikata irin wannan babban kuskure,” kamar yadda matar ta shaida wa jaridar Al-Riyadh ta Saudiyya bayan ta bar gidan
Ta ce “duk da mijin nata ya nemi gafara kuma ya yi alkawarin ba zai sake yin hakan ba, amma ta dage cewa tana son a raba auren. “Domin ba shine namiji na farko a Saudiyya da ya zauna da matar da bai taba ganin ta ba, wasu sunyi kafi shi kuma sun zauna lafiya”
Taskar Labarai ta ruwaito matar na kawo misalai cewa “Akwai Ali al-Qahtani wanda matarsa ta kasance tana sanye da Nikaf tsawon shekaru goma na aurensu. Lokacin da ya yi ƙoƙarin cirewa sai ta yi barazanar barinsa dakyar ta zauna bayan ya yi rantsuwa da Allah ba zai sake gwadawa ba”
Ta kara da cewa “Ga Ummu Rabea al-Gahdaray nan shekarar ta 70 daga ya’yanta har mijinta shekara, ba su taba ganin fuskarta ba. Haka tsarin Al’adarmu yake, ya sani daga mahaifiya ta har ’yan’uwana haka suke kuma sai da ya yarda zai bi tsarin kafin aka daura mana aure” inji ta.
Da aka tambaye ta ta yaya ta haifi ‘ya’ya ba tare da mijinta ya taba ganin fuskarta ba, sai ta amsa da cewa: “Aure soyayya ce ba ganin fuska ba”
Taskar Labarai ta ruwaito yawancin kasashen Musulunci irin su Saudiyya da Iran suna bukatar mata su rufe fuskokinsu a bainar jama’a amma sukan bude a duk lokacinda suka kebanta a gidajensu ba a tilasta musu rufe fuska.
Duk Malamai sunyi ittifakin cewa lullube fuska da nikaf a koda yaushe – ko da a gaban mijinki ne – ba koyarwar Musulunci bace, sai dai kawai tsohuwar al’ada ce da wasu tsirarun mata ke yi a lungu da sako na kasashen Larabawa