Kannywood

Ba na tare da Rarara : baban chinedu yayi zazzafar martani ga rarara akan buhari

Fitaccen mawakin nan baban chinedu wanda yake abokin aikin dauda kahutu rarara ne wanda sun daɗe tare wajen rerawa tsohon shugaban kasa Muhammadu buhari wakoki tun shekarar 2015 har zuwa yanzu lokacin shugaban kasa bola Ahmed tinubu.

Dauda kahutu rarara yayi maganganu sosai akan zagin tsohon shugaban Muhammadu Buhari akan cewa baiyi komai ba, kai kwana dari 1000 na gwamnatin bola Ahmad tinubu yafi na shekara takwas 8 din buhari bayan da yake cewa babu wanda yayi aiki kamar tun kafuwar samun yancin najeriya a cikin wakokinsa.

Ba na tare da Rarara : baban chinedu yayi  zazzafar martani ga rarara akan buhari
Ba na tare da Rarara : baban chinedu yayi zazzafar martani ga rarara akan buhari Hoto/Dclhausa

Baban chinedu ya samu zan tawa da jaridar Dclhausa inda ya bayyana matsayar akan kalaman rarara ga tsohon shugaba Muhammadu Buhari ga abinda yake cewa:

“Ai idan na samu chanji shi ya samu ko kwata kwata chanjin sa ni na samu, ya samu chajin mana, shi yanzu ya isa yace bai samu chanji a rayuwarsa a gwamnatin general muhammadu buhari , sai dai ace ba’a samu yadda ake so ba wannan shine gaskiya.

Kuma muce gwamnatin buhari bata kyautatawa yan siyasa ba gaskiya ne, yan siyasa da yawa abinda sunkayi ba’a yi musu ba gaskiya ne, Allah yayiwa rarara rufin asiri idan yace bai yi masa ba yayi karya, ko munan bamu kai kwata kwata shi ba amma ya rufa mana asiri” inji baban chinedu

Mai tambaya : shin ko ka yarda da cewa abinda dauda yake cewa gwamnatin Muhammadu Buhari yayi damal damal da kasar nan?

“Ni ban yarda da wannan ba abinda yasa nace maka ban yarda da wannan ba a cikin gwamnati zaka samu wasu sunyi dai-dai wasu basu yi ba, a cikin gwamnatin buhari ko kaƙi ko kaso akwai abubuwan alkhairi da ya kawo a najeriya, wanda ba zaka ce wannan gwamnatin kwana dari ta kawo shi wallahi baka isa ba, irin wanann alfarma ai.

Wata rana akwai alfarma da za’a yi maka bana kuɗi bane ba kuma rarara yana da alfarma a kasar nan fiye da yadda kake tunani wani abu zai iya faru yaje kuma ayi mashi, amma nasan an ɓata masa rai magana ta gaskiya ni na sani anyi masa ba dai-dai ba an ɓata masa rai amma ya zamo mai hakuri kada ya yarda kayi fira da yan jarida kana fushi.”

Mai tambaya : wani minista ko wane mukami kake neman wanda idan an baka shine an saka maka irin gudunmawar da ka bada a wannan gwamnati?

“A bani shugaban kula da makabarta ni ba Shikenan iyakar ta a nan ba shida ba kuɗi ake bayarwa a baiwa gawa ba, amma ni a bani mukami da kar a bani abinda nake nema yana wajen Allah -inji baban chinedu.

Ga bidiyon nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button