Kannywood

Mahaifina bai amince fim ba sai da na Gamsar da shi da Ayar Alkur’ani – Nura Hussaini

Jarumin finafinan Kannywood, Nura Hussaini ya bayyana yadda aka yi ya gamsar da mahaifinsa har ya amince ya bar shi ya fara harkar fim.

A wata tattauna da BBC Hausa tayi da shi a shirin Daga Bakin Mai Ita, ya ce sai da ya janyo wa mahaifinsa ayar Al’Qur’ani wacce ta yi magana akan fadakarwa sannan ya amince.

Ya fara bayyana cewa mahaifinsa malami ne kuma a wurinsa yayi karatun addini har ta kai ga ya yi sauka sannan ya fara hadda.

Sannan a wurin mahaifiyarsa ya koyi littafan addini da dama. Ya bayyana yayi karatun boko a Kano bayan tasowa a garin Kano.LB na tattara bayanai

Ya ce a baya shi malamin Islamiyya ne don yana koyar da yara karatu. A ranar da ya fara ganin fim ne ya fara sha’awar shirin, a lokacin ya je koro yara don tafiya islamiyyarsa da yake yi tsakanin magriba da isha.Mahaifina bai amince  fim ba sai da na Gamsar da shi da  Ayar Alkur'ani - Nura Hussaini

Ganin yadda ake shirin fim din “Kara da Kiyashi” yasa yayi sha’awar shirin daga nan ya nemi sanin yadda abin yake.

Yayin gamsar da mahaifinsa ya fara da cewa:

Ina tsoron kada mahaifina ya ki amincewa in yi saboda zai ga cewa fim abu ne mai cinye lokacin karatu. Nace Malam na ga wani abu da ake yi wai shi fim. Kuma ina so in fara.

Amma bai gane ba saboda be ma san menene shi ba. Sai nace abinda ake nufi da fim shi ne ud’u ila sabili Rabbika bil hikmati wal mau’idhatil hassanati.

Sai yayi shiru, yace, ai wannan abu mai kyau ne. To sai naji dadi saboda abinda nake so shi ne in ji ya amsa.”

Ya ci gaba da bayyana yadda mahaifinsa yayi masa wasiyya da ya kasance mai tsare mutuncin kansa kamar yadda iyayensa su ka tsare nasa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button