Labarai
SAI BANGO YA TSAGE: Kisan ‘Kare Dangi Akan Musulaman Rohingya
A cikin kwanakin nan, mafi rinjayen al’umman kasar Burma sun kaddamar da kisan ‘kare dangi akan musulman Rohingiya na jihar Rakhine dake yammacin kasar. Sun kone sama da gidaje 700, wato kaso 99% na gidajen musulman, kana kuma sun kashe sama da mutane 400 (kuma suna cigaba da kashewa), yayin da sama da mutane 140,000 suka yi gudun hijira.
Bayyanannun hujjoji na nuni da cewa ba wai wasu tsiraru ne suka kaddamar da kisan gillar musulman ba, hukumomin tsaron kasar ne suka jagoranci kisan inda sauran al’umman su suka biyo baya. Kafar yada labarai ta Aljazeera ta ruwaito hukumar sojojin kasar ta Burma tana cewa ta kasha ‘mafadatan’ musulmai 370.
Kuma ba hukumar kasar ne kadai take wannan ta’addanci ba, sauran kabilu musamman mabiya addinin Buddha dake makwabtaka da Musulman na Rohingya sun bi sawun hukumomin kasar tasu.
Sun kasha mutane kisan wulakanci, wasu sun kona su, wasu sun musu sun sassare su, wasu sun musu duka har lahira, wasu sun harbe su, wasu an jefa su a teku da ran su. Sun kasha kananan yara kisan mugunta, sun kasha mata da tsofaffi kisan rashin tausayi, sannan sun kore su daga garin su, inda tarihi ya nuna suna da asali tun karni na 12.
Wadannan musulman Rohingya ba wai sub a ‘yan kasar Burma bane. Su kabila ne na musulmai da suke da tarihi a kasar ta Burma. Amma kasar ta Burma taki amincewa dasu cikin kabilu 135 da gwamnati ta amince dasu kuma an hana su katin zama dan kasa tun shekarar 1982, wanda hakan ya hana su samun jiha na kansu.
Bayan juyin mulkin shekarar 1962 a kasar ta Burma, hukumomin kasar sun bukaci kowani mazaunin kasar ya mallaki katin dan kasa. Amma su musulman Rohingya sai aka basu katin ‘yan kasan waje mazauna kasar. Wannan ya katse su daga samun manyan aiki da kuma ilimi.
A shekarar 1982, kasar ta fitar da dokan dan kasa wanda a karkashin dokar aka sake kin amincewa da Musulman Rohingya cikin kabilu 135 na kasar. Dokar ta sanya sharudda uku na zama dan kasa. Kafin a amince da mutum a matsayin dan kasa sai ya kawo alama da zai nuna ahalinsa sun kasance a kasar tun 1948, sannan kuma ya kasance ya iya daya daga cikin manyan yarukan kasar sosai. Da dama daga cikin Musulman Rohingya basu da wadannan takaddu saboda kodai dama babu su ko kuma an hana su.
Dalilin wannan doka, an tauye wa musulman Rohingya ‘yancin sun a karatu, aiki, tafiya, aure, yin addini da kuma samun kiwon lafiya. Bazasu iya yi zabe ba kuma akwai iyakoki da aka musu akan shiga yankunan kasar da kuma samun ayyukan yi Kaman likitanci, shari’a ko kuma tsayawa zabe a wancan lokaci.
Tun shekarar 1970, makamancin wannan kisan gilla yayi ta faruwa akan Musulman Rohingya na jihar Rakhine wanda hakan yasa dubbai daga cikin su suka yi hijira zuwa Bangaladash da Malashiya.
Ko a watan nuwamban shekarar da ta gabata (2016), wani jami’in majalisar dinkin duniya ya kalubalanci gwamnatin Burma da yin abunda ya kira “shafe kabila daga doron kasa”, wannan kuwa ba shine karo na farko da aka kalubalanci gwamnatin Burma da yin hakan ba.
Duk da cewa gwamnatin kasar ta yanke alakan ‘yan jarida da jihar ta Rhakine, inda garin Musulman Rohingya yake, bayanai sun nuna cewa jami’an tsaron kasar ne suka fara kaddamar da kisan ‘kare dangi akan Musulman Rohingya, inda jami’an suka bada dalilin yin hakan da wani hari da aka kai barikin ‘yan sandan dake yankin.
Mai karatu zai fahimci cewa, wannan kisan da yake gudana a Rakhine ba fada ne tsakanin kabila da wata kabila kawai ba. Kisan ‘kare dangi ne da gwamnati tare da hadin gwiwar jama’ar gari suka kaddamar akan musulman Rohingya musamman saboda dalilai na tsohuwar kiyayya da suke dashi ga musulman.
Wannan yasa dole manyan kasashen musulmai masu fada aji su fito don kawo karshen wannan ta’addancin taron dangi da ake yiwa musulmai a Burma ta hanyar samar da mafita na din-din-din.
Kasashe masu makwabtaka dasu kuwa, suyi gaggawan basu mafaka iya gwargwadon su. Kana kuma suyi kokari wajen inganta rayuwar su a matsayin sun a ‘yan adam kuma musulmai.
Hukumomin kare hakkin bil’adama da kuma majalisar dinkin duniya dole ta dauki matakin gaggawa akan wannan zalunci. Wannan kisan kiyashi da ya gudana dole ya zama na karshe, a zakulo jaruman wannan kisan gilla a kaddamar da hukunci a kansu a idon duniya don ya zama darasi ga masu talaucin tunani da sajewar basira.