Labarai

INEC ba za ta yi zaben gaskiya ba – Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya zargi hukumar zaben Najeriya INEC cewa ta shirya yin magudi a zaben 2019.
Obasanjo wanda ya dawo yana adawa da Buhari bayan ya goyi bayansa a zaben 2015, ya ce ko INEC ta shirya yin gaskiya gwanatin APC ba za ta bari ba.
Tsohon shugaban ya fadi haka ne a cikin wani dogon bayani mai taken “damuwa da kuma mataki” da BBC ta samu kwafi.
Sai dai zuwa yanzu babu martani da ya fito daga INEC da kuma bangaren gwamnatin APC wadanda Obasanjon ya zarga da shirya magudi a babban zaben da ke tafe a watan Fabrairu.
A cikin bayaninsa, Obasanjo ya kira APC da ke mulki a matsayin jam’iyyar INEC, saboda yadda take katsalandan ga harakokinta.
Obasanjo ya bada misali da zaben jihar Osun inda ya ce zaben da ba a kammala ba amma aka ce an kammala duk da hujjoji da suka tabbarar da akwai matsaloli a zaben.
“Hakan ya tabbatar da INEC na iya sanar da jam’iyyar da take so ta ci zabe ko da kuwa ta sha kaye ko kuma akwai matsaloli da za su iya sa a soke zaben ko ta ce sai an je zagaye na biyu,” in ji shi.
Karin bayani na tafe…

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button