Mustapha Nabaraska yayi martani akan bidiyon sa da yake Sallah


Wannan bidiyon da anka nuna Mustapha Nabaraska yana karatun Alkur’ani ya hada da hadisi a cikin babban masallacin da ke kasar Saudiyya shi da wani mutum abun ya jawo CeCe kuce sosai.
To shine mutane suke ta fadin wannan jahilci ne abunda ya aikata to amma daga baya yayi shiru sai yanzu yake gagawa duniya hujjarsa na yin wannan abun a cikin wani faifan bidiyo yake cewa.


“Malam Aminu an hada aya da hadisi to ae ba sallah ankayi ba, kuma idan bakayi haka ba ae bazasu dora ba, amma yanzu kaga suna ta cece kuce da chachar baki ba sallah ake ba cewa ankayi Allahu Akbar an girmama ALLAH kenan.
“Anyi fatiha an kawo aya an jawo hadisi anyi Allahu Akbar ae zamama zanyi ni ba sujjada ko ruku’u zanyi ba.
Malam Aminu ba sallah ankayi ba da farko ance Allahu Akbar an jawo aya da hadisi a karshe an ce Allahu Akbar an girmama ALLAH kenan.” Inji Nabraska.
Mutane sun to fa martani akan wannan bidiyon da shafin Instagram na jakaddiyar Arewa na wallafa.
@Young ustaz cewa yake :
Kaga to inda matsalan take dama shiru Nabraska yayi daya fi masa Alkhairi amma wannan a gani na kara kunna kaine a garin damage control.
Idan ba sallah ba me ake daidaitawa sahu har da rike hannu?
Wacce Ibadah ce daga Allahu Akbar ake fatiha?
Kuma fa bayan karatu har kayi Allahu Akbar? Da hakan ake kulle Addua?
Amma wannan damalmala ne kawai.
@Abdollahaliyu11 cewa yake :
Kaji jaki matsiyaci. Sallar ne abun dariyarka. Inbadon kar ace na zafafa ba wlh sai ince Allah tsinema albarka. Idan kiristoci sukayi sai ace suna wasa da sallah. Wannan abin bakin ciki ne wlh.
@nm_fabric_nd_more : cewa take :
Mtswww wannan ba abinda wasa bane ji da yake dariya saikacce wani sabon kamu,toh Allah abin wasanka ne da zaka rinka wasa da sallah kuma ka rasa ma inda zakayi saikaje masallaci me daraja,wlh ka tuba koh ma mene kayi laifi.kuma aje akara neman ilimin addini ba na magana ba.
@r_jisambo cewa yake :
Gaskiya Wannan mutumin ya tabbatar da kallon da ake masa, domin wannan abinda yayi yafi kuskuren ma da yayi a Sallar muni. Allah ya kyauta. Lallai muna neman karatun addini isash-she kuma ingantaccen, amman irin wannan hauragiya matukar mutum ya ginu a kanta kuma ya gina wasu, dasu dashi sun tafi kenan.
Ya Ubangiji ka tabbatar damu akan dai-dai.
@leemah7 cewa take :
Wani jahilci Wannan babu kunya ne ai saboda ba a wasa da sallah kuma ba a wasa da Allah





