Labarai

Kotu ta baiwa Natasha Akpoti matsayin wadda ta lashe kujerar sanata a kogi

Advertisment

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a Jihar Kogi ta soke nasarar Sanata Abubakar Ohere a matsayin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta tsakiya.

Haka kuma kotun ta ayyana Natasha Akpoti-Uduagan ta jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

Kotu ta baiwa Natasha Akpoti matsayin wadda ta lashe kujerar sanata a kogi
Kotu ta baiwa Natasha Akpoti matsayin wadda ta lashe kujerar sanata a kogi

Jaridar BBC Hausa na ruwaito jagoran kotun Mai shari’a K. A Orjiako ya ce an ƙara wa Ohere ƙuri’u a rumfunan zaɓe tara cikin ƙaramar hukumar Ajaokuta, yayin da kotun ta ce an rage wa Natasha ƙuri’u da gayya a hukumar zaɓen da kuma wasu rumfunan zaɓe uku da ba a shigar wa Natashan ba a ƙaramar hukumar.

Bayan da kotun ta kammala tattara alƙaluman ne ta ayyana Natasha ta jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen bayan da kotun ta ce ta samu ƙuri’a 54,074, yayin da ta ce Sanata Ohere ya samu kuri’a 51,291

Natasha Akpoti-Uduagan tayi fustin da nuna yiwa Allah godiya akan nasarar da ta samu.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button