Kannywood

Shin da gaske yan Kannywood basa taimakon junansu a lokacin da sunka shiga wani mawuyacin hali ?

Advertisment

A makon nan, Kafafen sada zumunta ya dau zafi biyo bayan sakin videon da Zinariya ta yi na Mallam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Karkuzu. A videon, an hangi Karkuzu yana kwarototon neman taimakon bayin Allah da yan masana’antar Kannywood lura da makancewa da yayi Kuma bashi da muhalli. Wannan ya janyo hankulan mutane da duniya yayin da bayin Allah suka taimaka da taro da sisi domin ganin an taimaki Baba Karkuzu. Hasali ma, Dan wasan kwallon kafar Super Eagles Ahmed Musa MON yanzu haka ya siya mishi gida wanda zamu kawo muku cikakken rahoto akan lamarin.

Shin da gaske yan Kannywood basa taimakon junansu a lokacin da sunka shiga wani mawuyacin hali ?
Shin da gaske yan Kannywood basa taimakon junansu a lokacin da sunka shiga wani mawuyacin hali ? Hoto : Facebook/Instagram

Mu koma kan taken rubutun mu akan shin Kannywood suna taimakon yan uwan aikin su idan suka shiga mawuyacin hali?

Editan zinariya tv Auwal Saleh wanda ya san baba karkuzu kuma yi hira da shi, Baba Karkuzu ya tabbatar mai da cewa akwai yan masana’antar Kannywood wadanda ba zai manta da irin taimakon da suka mishi ba a rayuwa. Domin kuwa sun taimake shi yayin da yake jinyar idon shi wanda daga baya Allah ya kaddara zai makance.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid02kTSbZndjMmXxR7cZFYFL3cvkFWn6LeQnXEZr62fQZQR4r49tVv48uobZia752C8fl&id=100079860385774&mibextid=Nif5oz

Misali: Baba ya shaida min cewa jarumi Adam A Zango ya bashi 300K da kayan abinci. Ba wannan karon bane karon farko da Adam Zango yake taimakon shi. Har wa yau, Baba Karkuzu ya tabbatar min da cewa Ali Nuhu a lokuta mabanbanta ya turo mishi da taimakon Kudi da kayan abinci. Sannan uwa uba yar shi Hadiza Aliyu Gabon ya ce bai san sau nawa ta taimake shi ba. Yanzu haka akwai wasu jaruman Kannywood da muka yi waya da su suka shaida min cewa suna hanyar zuwa Jos domin ganin Karkuzu tare da bashi tallafin da Jaruman Kannywood suka hada mishi.

To ashe kun ga baza mu ce Yan masana’antar Kannywood basa taimakon yan uwansu ba kwata-kwata. Sai dai mu ce su kara kokari akan kokarin su.

Har yanzu dai kofar taimako a bude take domin taimakon Baba Karkuzu da Kudi ko kayan abinci. Batun gida kuwa, tuni an wuce wajen domin Ahmed Musa ya gwangwaje Karkuzu da gida.

3034702720
SHUAIBU ABDULLAHI
FIRST BANK
07036182052Ga lambar waya da account din Baba Karkuzu ga duk wanda zai taimaka mishi ko kuma ya kira shi kai tsaye

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button