Labarai

Fitar jini bayan jima’i ka iya zama alamar kansar mahaifa ce — Masani

Farfesa Isaac Adewole, tsohon ministan lafiya a Nijeriya, ya ce mutane da yawa ba su da masaniyar cewa fitar jini musamman a lokacin bayan kammala jima’i na iya zama alamar farko ta kansar mahaifa.jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito

 

Adewole, wanda da shi aka samar da cibiyar African Cancer Coalition, ya shaidawa manema labarai a Legas a yau Alhamis a wata hira ta wayar tarho cewa ana iya magani da kuma warkar da cutar sankarar mahaifa, idan an je asibiti kuma an gano ta da wuri.

Adewole ya ce: “Kalubalen da ake fuskanta a Najeriya, kamar kalubalen da ake fuskanta a Afirka da kuma kasashe masu tasowa da yawa, shi ne cewa mutane da yawa ba su san halin da ake ciki na kansar mahaifa ba.

“Saboda haka, ba sa zuwa asibiti har sai ciwon ya yi ƙamari saboda dalilai da yawa.

“Na farko, ba su san alamomin matakin farko ba wanda ya hada da zubar da jini musamman a lokacin jima’i.

“Abin da galibin mata masu irin wannan lamari sukan yi shi ne su nisanci mazajensu suna ganin cewa su suka jawo shi.

“Wataƙila sun yi tunanin hakan ya faru ne saboda rauni, da kuma wani nau’i na rauni. Kuma abin dubawa, idan sun yi haka, zubar jini zai daina amma cutar za ta ci gaba da ci gaba.

“Don haka, kafin su ankara, tuni cutar ta yi nisa.”

Ya bukaci gwamnatoci da masu ruwa da tsaki su kara wayar da kan jama’a kan cutar ta Sankara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button