Kannywood

Yanzu – Yanzu : Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Advertisment

Yanzu nan Majiyarmu ta samu labarin cewa wata koyu da ke birnin jihar kano ta aiki ta murya Ibrahim kunya Shahararriyar Yar Tiktok din nan kamar yadda shafin freedom radio kano sunka ruwaito da wannna labarin da yammaci yau.Yanzu - Yanzu : Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Kotun shari’ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari’a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

Advertisment

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button