Na Dena Yin fim- Inji Mustapha Nebraska (karanta dalili)
Jarumin Fina finan hausa Mustapha Nebraska ya shaidawa fans nashi cewa ya Dena yin films kuma ya fice daga cikin Kannywood har sai randa Allah ya kawo karshen gwamnatin Jihar Kano ta Ganduje.
Cikin wani faifen bidiyon da jarumin ya wallafa a shafin shi, yacce ya dauki matakin me sakamakon abinda akayiwa jarumi Sunusi Oscar
Idan za’a tuna an kama Oscar ne bayanda wasu suka Kai wasu maganganu da yayi na sukar Ganduje wajen wasu jami’ai inda tuni aka kaishi kotu daga nan aka zarce dashi gidan yari na Gorondutse
Jarumin ya zargi wasu Jaruman kannywood da cewa da sa hannunsu a cikin abinda ya faru ga Oscar amma bai bayyana ko suwaye ba.
Koda yake dai tuni wasu sun karkata wannan zargi zuwa ga jarumi Ali Nuhu. Domin ji karin bayyani Ku danna kan hoton domin jin daga bakin Mustapha naburaska.