Yan Sanda sunyi awon gaba da Murja kunya yar tiktok
Yanzu nan majiyarmu ta samu labarin kamun fitacciyar yar tiktok din nan wanda tayi fice sosai a kafar tiktok inda gidan radio freedom radio kano sun ka ruwaito wannan labarin inda suke cewa.


“Rundunar Ƴan Sandan jihar Kano ta kama fitacciyar mai barkwancin nan ta TikTok Murja Ibrahim Kunya.
Koda ya ke Ƴan sandan ba su yi ƙarin bayani ba, amma idan zaku iya tunawa a shekarar da ta gabata ne wani lauya ya shigar da ƙorafi inda yake neman da a binciki Murja da wasu fitattun mawaƙa da masu amfani da TikTok kan zargin ɓata tarbiyya.
An kama Murjar ne yayin da take tsaka da shirye-shiryen shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Ƙarin bayani zai zo nan gaba.”
Wanda mutane suna ta mamaki shin mi nenen murya tayi da yan sanda sunka kamata amma hausawa kance komai ya ruba ɗoyi yake .