Jarumi Bello Muhammad Ya Sake Musuluntar Da Wata Budurwa A Jos Bisa Wani Sharadi


Fitaccen jarumin nan a masana’antar Kannywood, Bello Mohammed Bello wato General BMB, ya sake Musuluntar da wata budurwa a falon gidan shi da ke garin Jos.
Kamar yadda ya ci alwashi tun a lokacin ɗaurin auren ta farko da ya musuluntar tare da aurar da ita, Bellon, ya yi shela akan duk wacce aka ji ta na son musulunta, a gaggauta kawo masa ita ya laƙana mata kalma.
To, da alama dai wannan ikirari na shi, ya fara jawo wasu ma, domin an samu wata budurwa ita ma ta bijiro da sha’awar shiga Addinin na musulunci. Kuma tuni jarumin ya karɓe ta, tare da ba ta kalmar shahada a falon gidan shi, a gaban matar sa da kuma wasu makwaftan sa.
Domin kallon bidiyon yadda jarumi Bellon ya ba ya Musuluntar da wannan Matashiyar Kirista,ga bidiyon nan sai ku kalla da Nagudu tv na wallafa a tashar ta.
https://youtu.be/zLIvwxNJRPo



One Comment