Kannywood

Bello Muhd Bello Yayi martani mai zafi kan Dr. Hussain kan Kamal Aboki da Awarwasa

Tsinanne La’ananne Jinin ka Ya hallata domin Ka shiga cikin Hurunin Ubangiji Martanin General BMB ga Dr. Hussain

Fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Bello Muhammad bello Wanda akafi sani sani da General BMB Ya fito yayi martani me Zafi akan Wani Malami a kafar sadarwa na TikTok me suna Dr Hussain bayan da yayi wata magana marar dani akan marigayi Kamal Aboki da Marigayi Abdulwahab Alhassan Awarwasa.

Bello Muhd Bello Yayi martani mai zafi kan Dr. Hussain kan Kamal Aboki da Awarwasa
Bello Muhd Bello Yayi martani mai zafi kan Dr. Hussain kan Kamal Aboki da Awarwasa

Maganar da dr Hussain yayi tayi Matukar batawa jaruman Kannywood rai, domin bayan rasuwar kamal aboki ne wani malami ya fito ya bayyana cewa Comedy haramun ne Wanda harma ya kawo Hadisi Akan hukuncin hakan.

Sai dai bayan maganar malamin mutane da dama hade da sauran yan Kannywood sunyi ca akansa inda sukaita maida masa da martani wasu ma harda zagi.

Mutane sun bayyana cewa bai kamata ace malamin ya fito yayi wannan maganar ba domin acikin irin bidiyoyin da marigayi kamal yayi a lokacin Rayuwar sa yawancinsu Abubuwane na fadakarwa hade da nuna Soyayya ga fiyayyen halitta annabi SWA.

Bayan cece kuce da akaita yi akan Maganar kamal sai kuma Allah ya kara karbar rayuwar wani jarumin me Suna Abdulwahab Alhassan wanda Akafi sani da Awarwasa, ana tsaka da jimamin Rasuwar sane sai kuma Dr Hussain ya kara sakin wata faifan bidiyon akansa inda yayi Maganganu marasa dadi wanda sukafi na Kamal aboki.

Hakan yasa da yawa daga cikin jaruman Kannywood Suka fito suka mayar masa da martani Wanda suka hada da Ibrahim sinana wanda akafi sani da dimbadis, Nana Izzarso, tare da Bello Muhammad bello Wanda shine ya bayyana cewa tabbas jinin dr Hussain ya hallata Domin ya shiga hurumin ubangiji Kasancewar Yana yiwa jaruman Hisabi ne Wanda kuma hurumin ubangiji ne ba nasa ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button