Labarai

Nan gaba za a yi takarar Kirista da Kirista a Nijeriya,cewar matar Tinubu

Advertisment

Uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce nan gaba ƴan Nijeriya za su ga an haɗa tikitin takarar kirista da Daily Nigerian Hausa

Ta ce takarar Musulmi da Musulmin na jam’iyyar ne zai sanya wani sabon salo a fagen siyasar kasar nan bayan 2023.

Uwargidan Tinubu ta bayyana haka ne a jiya Laraba, a yayin taron mata na kamfe ɗin shugaban kasa na jam’iyyar APC na Kudu maso Yamma da aka gudanar a Mobolaji Johnson Arena da ke Legas.

Nan gaba za a yi takarar Kirista da Kirista a Nijeriya,cewar matar Tinubu
Nan gaba za a yi takarar Kirista da Kirista a Nijeriya,cewar matar Tinubu

Ta ce, “Game da tikitin musulmi da musulmi, wannan shi ne zai haska fasalin siyasa nan gaba. Wani lokaci nan gaba, za mu sami tikitin Kirista kaɗai. Abin da Allah ya yi a ƙasarmu yana da ban mamaki.

Advertisment

“Ina kawo muku gaisuwar ban girma daga uwargidan shugaban kasa, mai girma Aisha Buhari. Ta aika da sakon fatan alheri da soyayya ga al’ummar Legas, haka ma ga gwamnan da ke sa zuba ayyuka a jihar Legas.

“Mun gode muku da kuka fito da yawa duk da kalubalen da ake fuskanta. Zuwa na nan kamar na dawo gida ne. Kimanin shekaru 23 da su ka gabata Allah ya albarkaci miji na ya zama gwamna, kuma na mara masa baya a matsayin uwargidan gwamna.

“Ina so in gode wa mutanen Legas ta tsakiya da suka aiko ni in wakilce su. Ni ce mace ta farko da ta zama Sanata sau uku. Wannan dama ce mai ban sha’awa, kuma na yi aiki don amfanin mutanenmu tun 2007 lokacin da mijina ya bar ofis.”

Ita ma da take jawabi a wajen taron, uwargidan gwamnan jihar Legas, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, ta yi kira ga matan jihar da su zabi jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Ta ce a wani bangare, “Alkawarin shugabancin Tinubu-Shettima shi ne cewa duk ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da shekaru, launi, jinsi, kabila, addini, ko siyasa ba, za a tallafa musu don cimma burinsu. Wannan shugaban kasa zai yi duk mai yiwuwa don kara wa mata dama a siyasa.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button