Barayin kaduna su godewa Allah ba Nine Gwamna ba, bazan tausayawa azzalumi ba – Shehu sani
A wani rahoto da munka samu a cikin wata fira da wani dan gwagwarmaya ya fitar cmrd abiyos Roni ya fitar da zantawar sanata Shehu sani da yayi adawa da wani bashi da gwamnatin nasiru El-rufai taci wanda yaki yarda da aciyo bashin a lokacin da yana sanata na tsakiya a jihar Kaduna.
Gwamnatin uba sani ta sanya ayi bincike akan yadda gwamnatin nasiru El-rufai ta ciyo bashi kuma ta kashe su ba bisa ka’ida ba.
Shehu sani yana cewa
“A shekarun baya na ja hankalin mutanen Kaduna da suyi hattara akan yadda gwamnatin take so ta sanya mu cikin wani rami da bazamu iya fita ba, a matsayina na wanda ya dade yana gwagwarmaya na daɗe da sanin irin waɗannan mutane kuma nasan abin da ake nufi da aƙida hari hujja, mune munka kawo wannan dimokuraɗiya a Nijeriya , mu muka yaki sojoji, mu a aka kama aka daure, mune munka sadaukar da kanmu wajen tabbatar da dimokuraɗiya a Nijeriya.
Duk da bamu cikin harka gwamnati mun san abin da yake tafiya a lokacin Nasiru ya tsoratar da mutane da yawa,yan kasuwa ya tsoratar da yan siyasa , ya tsoratar da samari ,ya tsoratar da ma’aikata,ya tsoratar da mata.”
Shehu sani yayi maganganu masu zafi ku saurare su a cikin wannan faifain sautin murya.