Kannywood

Datti Assalafy yayiwa Yan fim wankin babban Bargo akan Sheikh Idris Abdul’aziz Bauchi

Babban Malamin Musulunci dodon makiya Allah Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi ya jefa babban kalubale ga ‘yan film

Malam yace a nuna masa ‘dan film guda daya mai addini, indai dan film ne a nuna masa mutum daya mai addini yazo a masa interview, zamu tambayeshi menene addinin? Akwai addinin da babu bin shari’ah a cikinsa?

Wannan shine tambaya da kuma kalubale da Malam Dr Idris Abdul-Aziz ya jefa wa ‘yan film da magoya bayansu

Na ga wani wakilin ‘yan film ya fito yana mayar wa Malam raddi, har yana kokarin nuna cewa wai Malam yana da tabin hankali a kokarinsa na kare ‘yan film

Magana ta gaskiya duk mai addini idan ya tsaya ya kalli ‘yan film da kyau zai fahimci babu addini a tare da su

Shirya labarai na karya, da hada mata da maza rawa da waka baligai sanye da sutura irin na ‘yan iska wanda muke gani a tare da ‘yan film ba addini bane, kuma babu wanda zai shiga harkan ya kasance yana da addini

Malam ba yana kore Musulunci Musulman da suke harkan film bane, ana samun Musulmi amma marar addini, addini da ake nufi anan shine ka bi karantarwan Musulunci, kabi abinda shari’ah na Musulunci yace ayi da wanda shari’ah ya hana, wannan shine addini

Tabbas film ba harka bace ta addini, harkace da lalacewada iskanci da ruguza tarbiyya da shaye-shaye da bin mazan banza hotel

Allah Ka shiryar da suأمين

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button