Abinda Dr Idris Abdul’aziz Bauchi Yadi Kan Yan Fim Gaskiya Ne – Inji Adam A zango
Adam Zango Ya goyi bayan Sheikh Idris Abdulazeez bauchi Kan Sukar Yan Kannywood da Yayi
Kamar dai yadda kowa Ya sani tin makon daya gabata aketa cece kuce akan Maganar da fitaccen Malamin Addinin Musulunci nan yayi Watau Sheikh Idris Abdulazeez bauchi inda ya bayyana cewa duk Yan fim babu mai addini acikinsu duk jahilaine.


Jaruman Kannywood tare da Masana’antar baki daya domin tun kafin faruwar hakan dama malamai sun bayyana cewa Jaruman Kannywood bata Tarbiyyar al’umma sukeyi.
Hakan yasa Jarumi Adam Zango ya fito ya bayyana gaskiya akan cece Kucen da akeyi har hakan tasa mutane suka fahimce shi kuma aka yaba masa
Gadai Cikakkiyar Bidiyon bayanin da yayi nan kamar haka.
https://youtu.be/7CpCMuh8pHg
Daga cikin maganganu na jarumi yana cewa magana ta gaskiya itace
” Duk yarinyar da ta shigo masana’atar Kannywood fim to duk yadd iyayenta n bata tarbiya haka zatayi a Masana’atar Kannywood saboda idan har basu iya hana ta fim kai wani jarumi ko babba a Masana’atar baka isa ka bata tarbiya ba.
Adam Zango ya kara da cewa a kullum ina addu’ar Allah ya gaggauta fitar dani a cikinta kullum ina tabbacin wanda yake bina yasan nayi wannan addu’ar wajen shekara goma ko bakwai ,amma sai Allah ya cigaba da daukaka da budemin hanyoyi naci gaba da abinda nake a Masana’atar shiyasa na fahimci cewa Allah yafi ni sani shiyasa bai kawo fitata daga Masana’antar fim ba”