Uncategorized

Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Gina Makaranta Batare Da Sunanshi Ba

Wani al’amarin duniyar nan sai tsoro yake bani shi wannan mutum me yayi zafi haka bayan cigaba ne ya samesu amma Allah ya kyauta adamu tsiga shine ya ruwaito wannan labarin a shafinsa inda yake cewa.

Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Gina Makaranta Batare Da Sunanshi Ba
Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Gina Makaranta Batare Da Sunanshi Ba

“Wani magidanci a Ogun mai suna Segun Omotosho Ebenezer ya lakaɗawa matarsa ​​Bukola duka har lahira saboda ta ki miƙa masa makarantar da ta gina saboda ta saka sunan ta.


A cewar rundunar ƴan sandan jihar Ogun, wanda ake zargin da marigayiyar sun yi ta cece-kuce a kan kadarorin kafin ya lakaɗa mata duka har lahira.

A wata sanarwar da ƴan sandan suka fitar a ranar Litinin ɗin da ta gabata sun ce an kama mutumin ne bayan da ya gudu a lokacin da aka tabbatar da cewa shi ne ya kashe ta sandiyar dukan da ta sha a hannunsa.

Wanda ake zargin dai bai a sani ba, ashe marigayiyar ta aika da saƙon murya ga ƴan uwanta, inda ta sanar da su cewa mijin nata ya yi amfani da wani makulli ya buga mata a kai yayin da yake tsaka da dukan nata, kuma idan ta mutu to su sani mijin nata ne ya kashe ta.”

Wani labarin : Zamu mayar da APC tarihi a Najeriya – Sai mun bata wuta a cewar Naziru Sarkin Waka

Fitaccen mawaki kuma jarumi a masana’antar Kannywood Naziru Sarkin Waka ya bayyanawa duniya wasu dalilai dalilai da suka saka yace sai mun maida jam’iyar APC tarihi a Najeriya.

Mawakin yace kamar dai yadda kowa yake ji a jikin sa basai anyi wani dogon Turanci ba duba da yanayin tsammanin da mutanan Najeriya sukayiwa jam’iyar amma daga baya suka tarar da ba haka ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button